Wani lokaci a jiya Jumu'a ne aka bayyana cewar kungiyar nan ta ISIS ta bayyana daukar alhakin kai harin da aka bayyana a matsayin mafi muni da aka kai a cikin kasar.
Wannan kuma shi ne karon farko da kungiyar ta dauki alhakin kai harin da aka ce an ga jini yana ta malala a Masallaci, ga kuma gwawwakin mutane, abin dai babu kyaun gani.
A ranar Jumu’ar da ta gabata dai ne wasu mahara suka haka Boma-Bomai a babban Masallacin birnin San’a, suka kuma tayar da su a daidai lokacin da ake Sallah, inda kai tsaye aka bada labarain mutuwar mutane sama da 30,yawan mamatan kuma sai karuwa suke kama daga lokacin da harin ya auku zuwa yanzu.ABNA